Isa ga babban shafi
Faransa

Jean Castex ya bayyana farin cikinsa a shirin allurar rigakafin korona

Franministan Faransa  Jean Castex
Franministan Faransa Jean Castex REUTERS/Gonzalo Fuentes
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Jean Castex ya bayyana farin cikin sa ne yayin ziyara daya daga cibiyoyin yiwa al’umma rigakafin cutar dake gabashin kasar, yana mai cewa a baya Faransawa nada cikin wadanda ke dari-dari da alluran a kasashen duniya.

Talla

Gwamnatin Faransa da tayi ta shan suka danage da yadda Shirin allurar rigakafin ke tafiyar hawainiya ta kudiri aniyar kara azama wajen gaggauta Shirin.

A karshen watan Disamba ne dai Faransa ta fara yiwa al’ummarta alurar rigakafin, inda ta soma da wadanda ke gidajen gajiyayyu da kuma waɗanda ake ganin suna da hadarin harbuwa da cutar.

To sai dai, ba kamar maƙwabtanta na Turai ba, aikin rigakafin na jan kafa, a Faransar, domin kuwa kasa da kashi daya na ‘yan kasar tayiwa alluran, idan aka kwatanta da aƙalla 4.52 da Burtaniya tayi kamar yadda alkaluman Jami’ar Oxford ta nuna.

Ko da yake ministan Lafiyar kasar Olivier Véran ya bayyana cewa da gangan suke tafiyar da Shirin a haka, domin tabbatar da mutane fa’idojin alular rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.