Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta saka dokar hana fitar dare

Franministan Faransa  Jean Castex
Franministan Faransa Jean Castex Ludovic Marin/Pool via REUTERS
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Gwamnatin Faransa ta fitar da sanarwa dangane da sabin matakan da ta dauka dangane da yakin da take yi da annobar Coronavirus.Firaministan kasar Jean Castex ya sanar da cewa gwamnatin kasar ta saka dokar hana fitar dare kama daga ranar asabar 16 ga watan nan.

Talla

A yau Alhamis gwamnatin Faransa ta sanar da saka dokar hana fita kama daga ranar asabar 16 ga watan janairun nan a matakan da ya shafi yaki da cutar Coronavirus, annobar dake ci gaba da lakume rayukan jama’a kamar wutar daji.

Yawaitar mutanen da suka kamu da cutar a Faransa ,ya sa hukumomin kasar saka dokar hana fita daga misalin karfe shida na dare a wasu yankunan kasar .

Jean Castex da ya jagoranci taron manema labarai da nufin kawo karin haske dangane da sabin matakan da suka cimma a zaman wakilan gwamnatin kasar a yaki da cutar coronavirus ya jaddada cewa kama daga ranar asabar ,Gwamnatin Faransa ta aiwatar da dokar hana fita dare.

Yin haka zai taimaka don samun nasarar takaita yaduwar cutar a kusan kantomomi 25 kamar dai yada daya daga cikin jami’an jam’iyya mai mulkin kasar Stanislas Guerini ya sheidawa manema labarai.

Wani binciken jin ra’ayin Faransawa na nuni cewa yan kasar sun gano da kuma sanin muhimanci matakan kariya daga kamuwa daga wannan cuta kamar dai yada hukumomin ke ta nanatawa duk da cewa wasu yan kasar na bayyana adawar su ga wani sabon tsari na kulle su mataki na uku har indan ta kama.

A duk kullum akala mutane 20.000 ne ke kamuwa da kwayar cutar coronavirus a Faransa,inda aka bayyana cewa a jiya ka dai mutane 23.000 ne suka harbu da kwayar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.