Isa ga babban shafi
Duniya-Coronavirus

China ta saka dokar ta bace a wani yanki sabili da Covid 19

Hoton sabon nau'in cutar coronavirus da ya bulla a kasar Birtaniya
Hoton sabon nau'in cutar coronavirus da ya bulla a kasar Birtaniya Twitter/@Reuters
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

China ta saka dokar ta bace a daya daga cikin biranenta kusa da birnin Beijing, mai dauke da mutane miliyan 5, matakin dake zuwa a yayin da jami’ai daga hukumar lafiya ta duniya WHO suka isa birnin Wuhan, makyankyasar covid19 dan gudanar da bincike a kan cutar.

Talla

An shafe kusan watanni biyu yankin na Wuhan ya kasance a killace, babu shiga babu fita, yankin da annobar coronavirus ta bulla.Wasu daga cikin kasashen Duniya kama daga Turai sun soma daukar matakan yakar cutar.

Ita ma Netherlands ta kara wa’adin dokar hana zirga zirga zuwa ranar 9 ga watan fabarairu mai zuwa a wani mataki na tsaurarar matakan hana yaduwar cutar, yayin da Switzerland ta amince da ingancin allurar riga kafin Moderna, bayan da ta kasance Kasa ta farko da ta fara amfani da Pfizer da Biotech da aka fitar kwanakin Baya.

A halin yanzu dai sama da mutane a fadin duniya miliyan 91,574,350 ne suka harbu da cutar, akalla miliyan 56,306,300 sun warke yayin da mutane kusan miliyan 2 suka mutu, kuma Amurka ke kan gaba da adadi mafi yawa…

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.