Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Mourinho ya koka da yadda 'yan wasansa suke gaza murkushe abokan hamayya

Jose Mourinho.
Jose Mourinho. REUTERS/Russell Cheyne
Zubin rubutu: Michael Kuduson
Minti 2

Kocin Tottenham,m Jose Mourinho ya koka da sakwa sakwan da ‘yan wasansa suka yi a wajen tsaron baya inda har suka bari Fulham suka taso daga baya suka buga kunnen doki 1-1 da su a daren Laraba, a wasan gasar Firimiyar Ingila, canjaras na 6 kenan da kungiyar ta arewacin Landan ta yi.

Talla

Sakamakon wasan Tottehanm da Fulham na daren Laraba yana da kamanceceniya da na wasanni da suka buga da Newcastle United, West Ham United da Crystal Palace, inda Tottenham din suka fara saka kwallo a raga, amma suka kasa rike wuta har aka farke.

Harry Kane ne ya fara ci wa Tottenham kwallo a wasansu da Fulham, amma dammamakin da ‘yan wasa, Pierre-Emile Hojbjerg da Son Heung-min suka baras suka sa Ivan Cavaleiro ya gasa musu aya a hannu bayan dawowa hutu.

Mourinho ya shaida wa wani taron manema labarai cewa sun samu damar 'yinta ta kare' a zubi na biyu na wasan amma suka yi sakaci, kuma har Fulham ta samu ta antaya musu kwallo daya a raga aka tashi ba kare bin damo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.