Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Lukaku ya cire wa Inter kitse a wuta

Romelu Lukaku dan wasan Inter Milan.
Romelu Lukaku dan wasan Inter Milan. Pool via Reuters/Martin Meissner TPX IMAGES OF THE DAY
Zubin rubutu: Michael Kuduson
Minti 2

Romelu Lukaku ya saka wata kwallo a raga da ka a karin lokaci a wasan zagaye na biyu na gasar cin kofin kalubalen Italiya a karawa tsakanin kungiyarsa Inter Milan da Fiorentina da aka tashi 2-1 a daren Laraba, lamarin da ya sa yanzu za su kara da AC Milan a zagayen kungiyoyi 16.

Talla

A minti na 119 Lukaku, dan kasar Belgium ya yi amfani da kwallon da Nicolo Barella ya kawo mai daga kusurwa, inda ya saka mata kai har ta wuce mai tsaron ragar Fiorentina Pietro Terracciano.

Tun da farko dan wasa Arturo Vidal, dan kasar Chile ya ci wa Inter Milan kwallo ana saura minti 5 a tafi hutun rabin lokaci Christian Kouame ya farke minti 12 bayan ab dawo hutu, abin da kenan ya kai wasan karin lokaci.

Daga benci Lukaku ya shiga fili a minti na 69, kuma ana saura minti guda a karkare wasan ya saka kwallo a ragar Fiorentina, kwallonsa ta 17 a dukkan gasasnnin wannan kaka, kuma wacce ta hana wasan kai wa bugun daga kai sai mai tsaron raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.