Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar wakilan Amurka ta tsige Trump a karo na 2

Donald Trump, Shugaban Amurka mai barin gado
Donald Trump, Shugaban Amurka mai barin gado MANDEL NGAN AFP
Zubin rubutu: Michael Kuduson
Minti 2

Shugaban Amurka mai barin gado, Donald Trump ya kafa tarihin  zama shugaban kasar na farko da majalisar wakilan kasar ta tsige a karo na biyu mako guda kafin kawo karshen wa’adin mulkinsa da ke cike da tada jijiyoyin wuya.

Talla

Majalisar wakilan kasar dake da rinjayen ‘yan jam’iyar Democrat ta kada kuri’ar amincewa da tsige shugaban, a karo na 2, kuma irinsa na farko a tarihi da yawan kuri’u 232 a kan 197 na wakilan dake goyon bayansa.

A zauren majalisar, ‘yan jam’iyyar Republican 10 ne suka goya wa takwarorinsu na Democrat baya, cikinsu har da kusa a jam’iyyar, Sanata Liz Cheney.

An zargi hamshakin attajiri, kuma shugaban Amurka mai barin gado, mai shekaru 74 wanda zai mika ragamar mulki a ranar 20 ga wannan wata na Janairu, da tunzura masu zanga zangar da suka mamaye majalisar dattawan kasar a ranar 6 ga wata domin hana tabbatar da zaben Joe Biden mai shekaru 78, al’amarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 5, ya kuma zubar da mutuncin demokradiyar Amurka.

Majalisar dattawan Amurka ba za ta yi zaman yanke hukunci a kan wannan al’amari kafin ranar 20 ga watan Janairu da Trump zai sauka daga karagar mulki ba, abin da hakan ke nufi shine attajirin zai tsallake rijiya da baya daga barin mulki ala tilas kafin cikar wa’adinsa.

Sai dai a nan gaba zai gurfana a gaban majalisar dattawar, inda idan aka tabatar da laifin da ya aikata, hukuncinsa ka iya zama haramta masa sake takarar shugabancin kasar a shekarar 2024.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.