Isa ga babban shafi

Faransa ta dawo da 'yayan Faransawa masu ikirarin jihadi gida

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron AP News
Zubin rubutu: Michael Kuduson
Minti 2

Faransa ta sanar da dawo da wasu yara bakwai daga iyalan mahara masu ikirarin jihadi, Faransawa, daga arewa maso gabashin Syria, a kokarinta na ci gaba da aikin dawo da su gida, wanda aka fara bayan ruguza daular musulunci.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce, tuni aka mika su ga hukumomin shari'a, kuma sashin zaman takewar al’umma zai  ci gaba da kulawa da su yaran, masu kimanin shekaru tsakanin 2 zuwa 11,.

Kananan yaran na daga cikin dubbun ‘yan uwa da iyalan mayakan IS dake wasu sansanoni yankin Kurdawa na al-Roj da al-Hol, tun bayan da aka ci karfin IS a Syria a shekarar 2019.

Kawo yanzu Faransa ta dawo da irin wadannan yara 35, yawancinsu marayu.

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama na ta matsawa gwamnatocin Turai lamba kan maido da yaran daga sansanonin kurdawa masu cinkoso zuwa cikin danginsu, yayin da Jami’an Kurdawa ke ta kira ga kasashe da su rabasu da yaran, suna mai cewa, basu da karfin kula da su na din-din-din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.