Isa ga babban shafi
Amurka

Zaman Majalisa kan shirin tsige Trump ya kankama a Amurka

Shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi da ke matsayin jagora a shirin na tsige Donald Trump biyo bayan tarzomar da ta faru a Capitol makon jiya..
Shugabar Majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi da ke matsayin jagora a shirin na tsige Donald Trump biyo bayan tarzomar da ta faru a Capitol makon jiya.. AP Photo/J. Scott Applewhite
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Majalisar Amurka na shirin kada kuri’a ta biyu dangane da shirin tsige Donald Trump mai barin gado a Laraba dai dai lokacin da mataimakinsa Mike Pence ya yi watsi da kiraye-kirayen amfani da tanadi kundin tsarin mulki wajen tsige shugaban dangane da tarzomar da ya haddasa cikin makon jiya a Capitol wanda ke matsayin babban abin Kunya ga Amurkan cibiyar Demokradiyya.

Talla

Mataimakin shugaban kasa Mike Pence ya yi watsi da bukatar da Nancy Pelosi ta mika masa na ganin ya yi amfani da sashe na 25 na tanadin kundin tsarin mulkin kasar wajen tsige Trump, matakin da ke zuwa dai dai lokacin da wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ke nuna cewa kashi 55 na Amurkawa na goyon bayan shirin tsigewar ciki kuwa har da jiga-jigan jam’iyyar Republican da suka hadar da Liz Cheney.

Trump wanda ke ci gaba da musanta cewa shi ne ya tunzura magoya bayan nasa a Larabar da ta gabata, har ta kai ga sun farwa ginin na Capitol mai kunshe da majalisun kasar, ya ce sam bai aikata ba dai dai ba yayinda ya kira yunkurin majalisun kasar na tsige shi a matsayin wani batu mai cike da ban dariya.

Zuwa yanzu dai kafar YOUTUBE mallakin Google ta bi sahun Facebook da Twitter wajen dakatar da Trump daga amfani da dandalin saboda abin da ta kira yunkurin tayar da rikici, bayan da shugaban ya sanar da sanya dokar ta baci tun a shekaran jiya Litinin gabanin rantsar da Joe Biden ranar 20 ga watan da mu ke ciki.

Haka zalika hukumar kare hakkin dan adam ta Human Right Watch ta roki shugaba mai jiran gado Joe Biden kan ya yi amfani da tanadin doka wajen ladabtar da Donald Trump kan abin da ya aikata bayan darewarsa karagar mulki a ranar 20 ga watan da muke ciki

Kungiyar ta Human Right Watch ta ce dole Trump ya fuskanci shari’a kan laifuka masu alaka da take hakkin dan adam, haddasa rikici da kuma tunzura jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.