Isa ga babban shafi
Birtaniya-China

Birtaniya ta yi kakkausar suka ga China kan azabatar da musulmin Uighur

Tsirarun musulmi 'yan kabilar Uighur kenan da ke fuskantar azabtarwa daga gwamnatin China mai bin tsarin burguzu.
Tsirarun musulmi 'yan kabilar Uighur kenan da ke fuskantar azabtarwa daga gwamnatin China mai bin tsarin burguzu. Johannes EISELE / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Birtaniya ta zama kasa ta farko da ta dauki mataki kan China game da cin mutunci ko kuma take hakkin dan adam da ake zargin kasar da aikatawa kan tsirarun musulmi ‘yan kabilar Uighur, inda a zaman zauren majalisar Dinkin Duniya, London ta yi kakkausar suka kan mahukuntan Beijing tare da barazanar kaurace sayen wasu kayakinta.

Talla

Birtaniyar ta bakin ministan harkokin wajenta Dominic Raab ta caccaki matakan da China ke dauka kan tsirarun musulmin ‘yan kabilar Uighur yayinda ta sanar da sabbin matakan ladabtar da China ciki har da daina sayen kayakin da kasar ke kai mata wadanda ake zargin ‘yan kabilar ake tilastawa gudanar da aikatau dinsu cikin mawuyacin hali da tagayyara.

Birtaniya wadda ta fara fuskantar tsamin alaka da China tun daga batun yankin Hong Kong cikin kakkausar murya Dominic Raab ya ce suna da cikakken hurumin tsoma baki don kawo karshen azabtarwa ga ‘yan Uighur, la’akari da cewa abi ne mai tayar da hankali da kuma bayar da mamaki ace har yanzu China na amfani da tsarin bautarwa kan tsirarun musulmin.

A cewar Raab, ci gaba da sayen kayakin na China musamman audugar da ake tilastawa ‘yan kabilar ta Uighur nomawa cikin mawuyacin hali, tamkar bayar da gudunmawa ne a bautar da dan adam da kuma take hakkokin tirarun musulmin da ke yankin Xinjiang a arewa maso yammacin Chinan.

Tuni dai Chinar wadda ta kulla sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da EU da za ta bata damar tallata kayanta a Turai ciki har da audugar da ‘yan kabilar ta Uighur ke nomawa cikin kaskanci da tilasci ta soki Birtaniya kan matakin na ta tare da musanta zargin bautar da tsirarun musulmin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.