Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta zartas da hukuncin kisa na farko cikin shekaru 68

Lisa Montgomery dattijuwar da kotu ta zartaswa hukuncin kisa a Amurka.
Lisa Montgomery dattijuwar da kotu ta zartaswa hukuncin kisa a Amurka. Reuters
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Kotun kolin Amurka ta bayar da umarnin zartas da hukuncin kisa kan Lisa Montgomery duk da bayanan da ke bayyana shakku kan cikakkiyar lafiyar kwakwalwarta, hukuncin da zai zama irinsa na farko da kasar ta yanke tun bayan 1953.

Talla

Kotun wadda ke kokarin bin umarnin Donald Trump wajen tabbatar da dawo da hukuncin kisa gabanin karewar wa’adinsa nan da kwanaki 7 masu zuwa, ta umarci gidan yarin da ke tsare da Montgomery mai shekaru 52 da ya zartas mata da hukuncin ta hanyar yi mata allurar guba da za ta saukaka mutuwa.

Lisa Montgomery, wadda kotu ta samu da laifin kisan wata mata mai juna biyu tare da sace dan cikinta a shekarar 2004, lauyanta Kelley Henry ya bayyana hukuncin a matsayin mai cike da rashin adalci.

Tun a shekarar 2007 ne kotu ta samu Montgomery da laifin kisa tare da satar yaro inda aka yanke mata hukuncin kisa amma kuma lauyoyin da ke kare ta suka daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.