Isa ga babban shafi
Afrika

Yan Uganda na dakon sakamakon zaben kasar

Akwatin zabe a kasar Uganda
Akwatin zabe a kasar Uganda AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Yau Alhamis yan kasar Uganda suka kada kuri’a a zaben shugaban kasa dake hada yan takara 11, sai dai adawar tafi zafi tsakanin matashin mawakin Raga Bobi Wine da shugaba mai ci Yuweri Museveni wanda ya share shekaru 36 kan mulki kuma yake neman sabon wa’adi na shida.

Talla

Yan sa’o’I da rufe ruhunan zabe a kasar Uganda, kungiyoyi na cigaba da bayyana damuwa kasancewa hukumomin kasar sun katse layukan sadarwa na intanet, bayan zazzafar yakin neman zaben da ya haddasa kame da mutuwar mutane 54 a wannan kasa ta Uganda dake yankin Afrika ta gabas.

Yan lokuta bayan ya kada kuri’arsa Bobi wine dan takara mafi zama barazana ga shugaba mai ci Yuweri Museveni yayi kira ga al’umma da su fito masu yawa don tabbatar da canji a wannan kasa, yayin da ya koka da jinkirin da aka samu a wasu runfunan zaben na babban birnin kasar kampala, lamarin da ya haddasa dogon layi.

Rahotanni na nuni cewa an fuskanci matsala a ruhunan zabe bangaren wasu na’urorin tantance masu kada kuri’a .

Wasu daga cikin wakilan jagoran yan adawa Bobi Wine a yankuna 22 sun fuskanci barazana da safiyar yau daga yan sanda da sojoji , kimanin yan kasar miliyon 18 suka kada kuri’unsu a runfuna dubu 34.600 da aka yi tanadi, hukumomin kasar sun hana taron gangamin yan adawa saboda rigakafin cutar korona, lamarin da ake ganin cikas ne ga yan adawar yayi da shugaba Museveni ke amfani da kafafen yada labarai na gwamnati.

Akalla mutane 54 ne suka rasa rayukansu kama daga farkon yakin zabe zuwa ranar kada kuri’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.