Isa ga babban shafi
Afrika

An soma kidayar kuri’u a Uganda

Wasu daga cikin masu zabe a Uganda
Wasu daga cikin masu zabe a Uganda REUTERS/Baz Ratner
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

An soma kidayar kuri’u a Uganda bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun da ya gudana a jiya Alhamis, wanda aka fafata tsakanin shugaba Yoweri Museveni dake neman wa’adi na 6, da kuma jagoran ‘yan adawa Bobi Wine da ya rikide daga mawaki zuwa dan siyasa.

Talla

Kafin zaben shugabancin kasar na Uganda dai an yi ta samun rikice-rikicen siyasa da masu bibiyar lamurran kasar suka bayyana da mafi muni cikin shekaru da dama, la’akari da cewar sama da mutane 50 suka rasa rayukansu yayin arrangama da jami’an tsaro, wadanda kungiyoyin kare hakkin dan adam ke zargi da yin amfani da karfi, wajen hana ‘yan adawa yakin neman zabe da kuma kame jiga-jigai daga cikinsu.

Gabannin zaben na jiya, gwamnatin Uganda ta bada umarnin katse layukan sadarwar Intanet a daukacin kasar, yayinda kuma a yanzu ake dakon sakamakon zabe cikin fargabar tashin sabon rikici, idan jami’an tsaro suka hana magoya bayan jagoran ‘yan adawa Bobi Wine sa ido kan tattara sakamakon kuri’un da aka kada.

Sama da mutane miliyan 18 suka cancanci kada kuri’a a zaben na Uganda, kuma dole dan takara ya lashe sama da kashi 50 na kuri’un da aka kada don kaucewa sake zaben zagaye na biyu.

‘Yan takara 9 ne suka fafata a zaben jiya ciki har da Shugaba mai ci Yoweri Museveni dake kan mulki tun shekarar 1986 da kuma fitaccen mawaki Bobi Wine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.