Isa ga babban shafi
Afrika

Ranar tuni da juyin juya halin Tunisia

Wasu daga cikin iyalan da suka rasa nasu a juyin juya halin Tunisia
Wasu daga cikin iyalan da suka rasa nasu a juyin juya halin Tunisia AFP/Fethi Belaid
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Yau Alhamis al’ummmar Tunisia ke cika shekaru 10 da yin zanga-zangar da ta zama juyin juya hali na farko a kasashen Larabawa, wanda ya kawo karshen mulkin shekaru 23 na shugaban kasar a waccan lokaci, Zine El Abidine Ben Ali.

Talla

Ranar juyin halin ta Tunisia a bana tazo ne a daidai lokacin da gwamnati ta killace daukacin al’ummar don dakile yaduwar annobar Korona, cutar dake cigaba da hauhawa bayan sake barkewar ta a karo na biyu.

Sauyin gwamnatin da a aka samu a Tunisia ya samo asali ne bayan da wani mai sayar da kayan masarufi Muhd Bouazizi ya cinnawa kansa wuta ya kuma mutu, sakamakon hana shi gudanar da sana’arsa da jami’an tsaro suka yi, abinda ya janyo boren day a rikide zuwa juyin juya halin day a tilastawa shugaba Zine El Abidine Ben Ali tserewa zuwa Saudiya har mutuwa ta cimmasa cikin shekarar 2019 a birnin Jiddah.

Kawar da gwamnatin Ben Alin dai ya haddasa makamancin yunkurin a wasu kasashen Larabawan dake arewacin Afrika da kuma Gabas ta Tsakiya, to amma juyin juya halin Tunisia ne kawai ya samu nasarar sauya gwamnati ba tare da barkewar rikici ba, sai dai har yanzu kasar na fama da matsin tattalin arziki da kuma cin hanci da Rashawa, matsalolin da Alaa Talbi na kungiyar kare hakkokin ‘yan Tunisia kan ingantacciyar rayuwa yace sai sun ga abin ya turewa buzu nadi akai.

A shekarar bara kididdiga ta nuna tattalin arzikin Tunisia ya durkushe da kashi 9 cikin dari, zalika kaso 1 bisa uku na matasan kasar basu da aikin yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.